Tapswap code 14 July....

Babban Bankin Argentina na shawarar sanya hoton
gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya a 2022,
Lionel Messi a kan takardar kudin ƙasar na peso 1,000.
A cewar Daily Mail jiya Alhamis, jaridar Argentina, El
Financiero, ta bayyana cewa babban bankin ƙasar
Argentina na son ya kafa wani abu na tunawa da
nasarar da tawogar ƙwallon ƙafar ƙasar ta samu a
Qatar,
mai cike da tarihi kuma tun kafin wasan da ta
samu nasara kan Faransa a ranar Lahadi ba kin ke
tunanin kan hakan.
A wani cikakken bayani da jaridar ta EF ta wallafa,
cewa muhimmin bangare na dalilin da ya sa a ke
tunanin sanya hoton Messi a jikin kuɗin peso 1,000 shi
ne cewa lambar rigarsa ta Argentina lamba 10 ce.
A tsarin kuɗin, za a saka fuskar Messi a gefe ɗaya,
inda gefe ɗaya kuma za a rubuta sunan tawogar ƙasar
‘La Scaloneta’ shine da aka tsara a bayan takardar
kuɗin.
Kalmar ta zama daidai da wannan rukunin tun lokacin
da Lionel Scaloni ya gaji Jorge Sampaoli a 2018.
Messi ya jagoranci Argentina ta doke Faransa a gasar
cin kofin duniya ta 2022 a karon farko tun 1986.
Comments
Post a Comment