Tapswap code 14 July....

Abduljabbar Ba tare da bata Lokaci ba Cewar Kungiyar
Harkar Musulunci Karkashin Jagorancin Sheikh Zakzaky
Kamar Yadda Jaridar Dokin Karfe TV ta ruwaito.
Wata Kungiyar harkokin Addinin Musulunci Kenan
Karkashin Jagorancin Sheik Zakzaky ta Gargadi cewa Ayi
gaggawar Sakin Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara wanda
aka Yankewa Hukuncin Kisa ta Hanyar rataya bayan da
aka kamashi da laifin batanci ga fiyayyen halitta annabi
SAW.
Tun dai bayan yanke wannan hukunci almajiran na Sheikh
Abduljabbar suka bayyana cewa basu yadda da Hukuncin
da aka Yanke masa ba don haka Zasu daukaka Kara.
Mutane da dama harda wasu manyan malamai sun
bayyana Hukuncin da aka yankewa Sheikh Abduljabbar
Nasiru Kabara Bai dace ba.
Hakan yasa yanzu kuma Kungiyar Harkar Musulunci
Karkashin Jagorancin Sheikh Zakzaky ta furta cewa ayi
gaggawar Sakin shi ba tare da bata Lokaci ba kamar
Yadda Jaridar Dokin Karfe ta ruwaito.
Comments
Post a Comment