Na Dakatar Da Haihuwa Haka, a Cewar Wani Mai Mata 12 Da ‘ya’ya 102 Da Kuma Jikoki 568

 Wani manomi ɗan kasar Uganda wanda ke da yara 102

da jikoki 568 da ya samu daga matansa 12 da ya aura

ya yanke shawarar daina haihuwa.

Ɗan kasar Ugandan mai suna Musa Hasahya mai kimanin

shekaru 67 a duniya ya bu kaci matansa da su fara amfani

da magungunan hana daukar ciki don su samu su din ga

cin abinci.




Jaridar The Sun ta rawaito Musa yana cewa: “Kudaden

shigana na kara yin baya a ‘yan shekarun nan saboda

tsadar rayuwa kuma iyalina na kara haɓɓaka. Ina ta auren

mata ɗaya bayan ɗaya. Ta yaya namiji zai gamsu da

mace daya. Dukkaninsu matana nawa na zaune ne tare a

gida ɗaya. Ya fi mun saukin lura da su da kuma hana su

hulɗa da sauran maza a kauyen nan.”

Zulaika wacce ta kasance amarya ga Musa Hasahya ta

ce ta haifa masa ‘ya’ya 11:

“Ba zan sake haihuwar ‘ya’ya ba. Na ga mummunan

yanayi na rashin kuɗi kuma yanzu ina shan maganin hana

ɗaukar ciki.”

Musa da iyalinsa gaba ɗaya na zaune ne a Lusaka da ke

kasar Uganda inda aka halasta auren mata da yawa. Sai

dai kuma akwai takaddama sosai game da shan

kwayoyin hana ɗaukar ciki kuma a kan alakanta shi da

lalata.

Kimanin kaso uku na yaran Musa suna rayuwa da shi ne

a cikin gonarsa.

Karanta Wannan Labaranin:

Wani Ɗan Najeria Ya Ɗauki

Tsattsauran Mataki Kan

Mahaifinsa Saboda Yaƙi Goyon

Bayan Ɗan Takarar Labour

Party

Shekarun ɗan autan Musa shida sannan dansa na fari

yana da shekaru 51 wanda ya girmi amaryarsa Zulaika da

kusan shekaru 21.

Yanzu baya iya aiki saboda rashin lafiya kuma biyu daga

cikin matansa sun rabu da shi saboda matsalar rashin

kuɗi.

A wani labarin kuma majiyarmu ta jiyowa Jaridar

Dimokuraɗiyya cewar, ana tsaka da ɗaurin aure, wata

amarya ta hau sama ta duro tace sam ita bata san wanda

ake shirin daura musu auren tare a daidai lokacin da

limami cocin ke shirin daura masu aure a coci.

Comments

Popular posts from this blog