Gasar Ƙwallon Ƙafa Ta Mata
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Saudiyya, SFA, za ta karɓi baƙuncin gasar sada zumunta ta ƙwallon ƙafa ta mata zalla a sabuwar shekarar 2023.
Ƙasashen Pakistan, Comoros, Mauritius da Saudiyya ne za su fafata a gasar.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da SFA ta fitar ranar Alhamis.
Za a gabatar da gasar ne a Filin Wasa na Yarima Saud bin Jalawi dake Al-Khobar a Lardin Gabashin Saudiyya daga 11 zuwa 19 ga Janairu, 2023.
Wannan dai yana daga cikin muradun da Sashen Mata na SFA ya sa a gaba don ƙarfafa gwiwar Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Mata ta ƙasar wadda aka kafa a bara.
Lamia bint Ibrahim bin Bahian, wata mamba a SFA ta ce an samu gagarumin ci gaba a ɓangaren ƙwallon ƙafa ta mata a ƙasar ta hanyar shirya gasar cikin gida ta mata zalla wadda ta sa aka gano yara masu baiwa a ƙwallon ƙafa.
Ta ƙara da cewa SFA ta yi amfani da dukkan matakai don bunƙasa ƙwallon ƙafa ta mata.
Bin Bahian ta ce wasan sada zumuntar da za a yi zai zaburar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasar ta shiga wasu gasa a nan gaba
Comments
Post a Comment