Tapswap code 14 July....

Odero ya bar malamin addinin cikin mamaki bayan ya
gabatar da bukatarsa
– Tsohon ya bukaci Ezekiel da ya taimaka masa da matar
aure, yana mai cewa mata biyu da ya fara aura sun bar shi
sannan ya sake auren wasu biyu amma suka mutu
– Mutumin wanda ke zaune a yanzu babu aure ya ce yana
neman dattijuwa yar shekaru 52 zuwa 59 kuma wacce ta
daina haihuwa don so yake ya hole a karshen rayuwarsa
Kenya - Wani dattijo mutumin kasar Kenya ya yiwa cocin
Fasto Ezekiel Odero da Mavueni, Kilifi tsinke sannan ya
bukaci malamin addinin da ya yi masa addu'an samun
matar aure.
Tsoho Ya Bige Da Rokon Malamin Addini Kan Ya Aura
Masa Mata Ta Biyar, Bidiyon Ya Haddasa Cece-kuce Hoto:
New Life Church.
Fasto Ezekiel ya cika da mamaki bayan mutumin ya roke
shi mata
Mutumin wanda kansa ke cike da furfura ya ba Ezekiel
labarin yadda ya auri mata hudu a baya amma a yanzu ya
saura babu mace.
Budurwa Mai Tallan Tuwo a Najeriya Ta tsallake, Ta Tare
Da Mijinta a Turai, Sun Bar Jama'a Baki Bude
Dattijon ya bayyana cewa matasan biyu da ya fara aura sun
rabu da shi sannan ya sake auren wasu biyu amma su
dukka suka mutu kuma yanzo yana neman wacce za su yi
rayuwa tare.
Faston wanda ke auren Fasto Sarah ya tambaye shi : " Shin
kana son sabuwar mata?"
Sai dattijon ya amsa da:
"Eh, ina son sabuwar mata amma bana son wacce za
ta haihu. Ina son dattijuwa tsakanin shekaru 52 zuwa
59. Wacce ba za ta zo da tarin bukatu ba don yarana
su iya daukar dawainiyarmu mu biyu."
Ya kara da cewar:
"Ba na son samun karin 'ya'ya saboda bani da sauran
fili da zan basu kuma ba zan iya daukar dawainiyar
makarantarsu ba. Kawai ina son matar da zan iya
more rayuwa tare da ita cikin farin ciki."
Himma Ba Ta Ga Rago: Gurgu Ya Mayar Da Kekensa Ya
Zama Shagon Siyar Da Kaya a Bidiyo
Bukatar da mutumin ya gabatar ya bar Ezekiel da
mabiyansa cikin mamaki.
Da dama sun cika da mamakin bukatar da mutumin ya
gabatar, inda wasu ke cewa zuwa neman shawara da
addu'a a wajen Ezekiel kuskure ne don baya goyon bayan
auren mata da yawa da na masu tazarar shekaru.
Magidanci mai yara 102 na fama da rayuwa
A halin yanzu, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wani dattijo
mai shekaru 67, Musa Hasahya, wanda ke zama a Lusaka,
Uganda, ya bayyana cewa yanzu baya so ya sake haihuwa .
Manomin ya yanke shawarar ne bayan ya haifi yara 102 da
jikoki 568 daga mata 12.
Comments
Post a Comment