Tapswap code 14 July....

Jihar Kano na neman Gwamnan da zai sake sauya fasalin manya da kananan titunan Kano birni da kauye. Gwamnan da zai sauya fasalin kasuwanni da tashoshin mota da kuma filayen wasanni da gutaren shakatawa.
Jihar Kano na na neman Gwamnan da zai sauya fasalin fasalin makarantu da harkar ilimi da sauya fasalin asibitocin Kano da harkar kiwon lafiya tun daga tushe.
Jihar Kano na neman Gwamnan da zai sauya fasalin birnin Kano ya kasance daya daga cikin birane masu tsafta da ban sha’awa ta hanyar shuka bishiyu da furanni a inda ya dace domin dacewa da da manyan buranen Afurka ta fuskar Kasuwanci da walwala da kuma zamantakewa.
Jihar Kano na neman Gwamnan da zai sauya fasalin harkar sufuri a cikin birnin Kano ya dace da zamani, a kuma sauya fasalin harkar tafiye tafiye zuwa gari gari.
Jihar Kano na neman Gwamnan da zai gina Kano da al’ummar Kano ba gina gadolinium a tsakiyar tituna masu fama da ramuka ba. Maganar gaskiya muna neman Gwamnan da zai sanya Kano a gaba domin kaita zuwa ga mataki na gaba.
Jihar Kano na neman Gwamna Gwamnan da zai tsara tare da kawata birnin Kano tare da samar da wasu manyan birane a sabbin masarautun Kano guda hudu.
Jihar Kano na neman Gwamnan da zai farfado da kananan hukumomi ya basu kudadensu domin yiwa al’umma birni da kauyula ayyuka raya kasa.
Jihar Kano na neman Gwamna wanda zai daukaka martabar addini da bin dokokinsa a tsakanin alumma, Gwamna wanda zai sanya Kano ta zama cibiya kuma jagorar addini mai tsafta a Arewacin Najeriya.
Jihar Kano na neman Gwamna mai gaskiya da tsoron Allah mai kokarin bin koyarwar addini da sanin ya kamata.
Wannan Gwamna ne a masu neman takarar Gwamnan a Kano zai iya ciyar da Kano gaba haka?
Yasir Ramadan Gwale ya rubuto daga jihar Kano – Najeriya
Comments
Post a Comment