2023 dinnan anamin zagon kasa Amma ta Allah ba tasuba| TINIBU....


 2023: Ana yi min zagon kasa, amma ‘Ta Allah ba ta

su ba’, za mu yi nasara

-Tinubu

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai

mulki, Bola Tinubu, a ranar Larabar da ta gabata ya yi

zargin cewa ana shirin yin magudi a babban zaben

kasar.

A ranar 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris ne

za a gudanar da zabukan na tarayya da na jihohi.

Amma yayin da yake jawabi a babban filin wasa na

Moshood Abiola International Stadium, Abeokuta, jihar

Ogun, Tinubu ya ce akwai wasu da ke kokarin ganin ba

a yi zabukan a wadannan rana ba, wato suna son su

kawo cikas ga zabukan.

Tinubu ya ce karancin man fetur da ake fama da shi a

fadin kasar nan da kuma sake fasalin kudin Najeriya

wato Naira na daga cikin shirin yi wa zaben zagon

kasa.

Sai dai ya tabbatar wa magoya bayansa, wadanda

dubbansu suka halarci gangamin, cewa ba za a iya

hana wannan zabe ba ko nasarar sa a zaben ba.

Wannan zabe gwagwarmaya ce, kuma jihadi, za mu

karbi mulki daga hannunsu, ba sa son a yi zabe, amma

ba za mu yarda ba, suna son fakewa da karancin man

fetur don haddasa rikicin ta yadda za a samu. ba za a

yi zabe ba,” in ji Tinubu.

Ko da man fetur ko babu, za mu yi zabe. Ba tare da

man fetur ba, za mu yi zabe. Kun san ni sosai, za mu

yi nasara, za mu karbi ragamar mulki daga hannunsu.

Za mu hadu aii a ranar zabe.

Manyan jiga-jigan APC a jihar duk sun halarci taron

gangamin da suka hada da tsohon gwamnan jihar

Gbenga Daniel, tsohon kakakin majalisar tarayya, Dimeji

Bankole da dai sauran su.

Comments

Popular posts from this blog