Ansako magoya bayan Arsenal da aka kama kan murnar sunci Manchester united|


 An saki magoya bayan Arsenal takwas da aka kama a

garin Jinja na Uganda, lokacin da suke murnar nasarar

da ƙungiyarsu ta samu a wasan hamayya da

Manchester United a gasar Premier Ingila.

Lokacin da aka kama su a ranar Litinin, suna sanye da

rigunan Arsenal da kuma wani kofi a hannunsu.

'Yan sanda sun ce babu wanda ya basu umarnin yin

wannan murna wadda za ta iya haifar da rikici a cikin

al'umma.

Kakakin 'yan sanda na yankin James Mubi, yace bayan

wata tattaunawa da aka yi tsakanin jami'an tsaro, an

amince a sake su kowa ya kama gabansa amma an

ginda ya musu sharuɗa.

Ɗaya daga cikin magoya bayan ya faɗawa 'yan jarida

cewa "sun nemi umarni gabanin wannan murna da suka

gudanar da nasara kan Man United".

Comments

Popular posts from this blog