Dole mu tabbatar da cewa muna noma abin da zamuci har mu fitar kasar waje..| BUHARI....


 Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ya umarci

shugabannin ƙasashen Afirka da su mayar da hankali

wajen ƙara bunƙasa harkokin noma a nahiyar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban

ƙasar Femi Adesina ya fitar ya ce shugaba Buhari na

jawabin ne a taron harkokin noma da shugabannin

kasashen Afirka ke halarta a birnin Dakar na ƙasar

Senegal.

Buhari ya yi kira ga takwarorinsa shugabannin ƙasashen

Afirka da su rungumi sabbin tsare-tsaren noma domin

tabbatar da samar da abincin da zai ciyar da nahiyar

har a fitar da shi zuwa ƙasahen ƙetare.

A yayin da duniya ke fuskantar hauhawar farashin kayan

abinci sanadiyyar yaƙin Ukraine, musamman kan alkama

da masara, shugaban na Najeriya ya zayyano wasu

matakan da ya kamata shugabannin Afirka su ɗauka

domin sauya wannan matsala.

'‘Ciyar da Afirka wajibi ne. ‘‘Dole mu tabbatar da

cewa muna ciyar da kanmu a yau da gobe da ma

kuma nan gaba. Abin da za mu fara yi shi ne mu

haɓaka harkokin noma a ƙasashenmu'', in ji Buhari

''Wannan na buƙatar samar wa manoma abubuwan da

suke buƙata kamar ingataccen irin shuka da wadataccen

takin zamani da sabbin dabarun noma''.

‘‘Idan muna son yin nasara dole mu tallafa wa

manomanmu, babu shakka akwai buƙatar taimaka wa

manoma, amma ya kamata mu yi haka cikin gaskiya,

mu cire musu ɗabi'ar neman rance, a maimakon haka

mu tallafa wa manoma''.

‘‘Ya kamata ƙasashen Afirka su ƙara kauɗi a

ɓangaren noma a kasafin kuɗinsu, musamman zuba jari

domin samar da abubuwan da ake buƙata kamar

haɓaka bincike da samar da abubuwan more rayuwa

musamman hanyoyi da noman rani da kuma

makamashi'', in ji Buhari.

Comments

Popular posts from this blog