Labarai da dumiduminsa: an harbe wasu yahudawa su biyar a wajen bautarsu. πŸ‘‡πŸ‘‡


 Akalla mutum biyar sun rasa rayukansu bayan wani harin

bindiga da aka kai kan wani wurin ibadar Yahudawa da

ke gabashin birnin Kudus.

Rahotanni na cewa lamarin ya auku ne a unguwar Neve

Yaakov da misalin karfe 8:15 na dare agogon kasar a

ranar Juma'a.

Masu ayyukan agaji sun sanar cewa mutum 10 ne harin

ya rutsa da su, inda wasunsu ke cikin mawuyacin hali.

'Yan sandan Isra'ila sun ce an kashe dan bindigar, sun

kuma bayyana harin a matsayin na ta'addanci.

Sun ce mutum biyu na cikin mawuyacin hali, inda wasu

uku kuma suka sami raunukan da ba su da hadari ga

rayukansu.

Amurka ta yi tir da harin. Wani kakakin ma'aikatar waje ta

kasar Vedant Patel, ya ce "Muna tare da al'ummar Isra'ila

a wannan mawuyacin lokaci da suke fuskanta."

Comments

Popular posts from this blog