Mahaifiyar Abba Gida Gida Ta Taya Shi Murnar Cika Shekara 60 A Raye

 

Mahaifiyar Abba Kabiru Yusuf, ɗan takarar gwamnan jihar

Kano a jam’iyyar NNPP, ta taya shi murnar zagayowar

ranar haihuwarsa.

Abba Gida Gida ne ya bayyana haka a wani rubutu da ya

wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis.

“Ina karɓar sa albarkar mahaifiyata don murnar cikata

shekara 60 a yau.

“Ina gode wa kowa da kowa bisa addu’a da goyon baya da

ake ba ni. Za mu cim ma nasara tare”, in ji Abba Gida

Gida.

Comments

Popular posts from this blog