Mutane Sama Da 10 Sun Mutu A Wani Gidan Ca-ca Bayan Da Gobara Ta Tashi

 

GIDAN CA-CA A CAMBODIA

Akalla mutane sama da goma ne suka mutu a sakamakon

tashin wata gobara a wani gidan Caca dake jikin wani otal

dake kasar Cambodia akan iyakar kasar da Thailand.

Jami’an yansanda sun baiyana cewa daruruwan

mutane ne ke a cikin ginin lokacin da gobarar ta

tashi a gidan Cacar wanda ke a garin Poipet a ranar

Larabar data gabata.

Wasu faya-fayan bidiyo da suka karade shafukan

sada zumunta sun nuna yadda mutane suka rika

dirowa daga saman bene, A yayin da kafofin yada

labaran yankin suka ce da yuyuwar a samu karuwar

mutanen da suka mutu.

Comments

Popular posts from this blog