Yadda Wata Mata Mai Cutar ƙanjamau Take Hada Jininta da Tsobo take Siyarwa


 Matar ta bayyana hakan a wani shirin gidan rediyon

Wazobia FM mai suna MarketRunz a daren ranar Laraba.

Jaridar The Punch ta rahoto.

Mai gabatar da shirin ya nemi masu sauraro da su kira

waya su bayyana abinda suka yi a kasuwa wanda

mutane basu sani ba wanda kuma ba su ji daɗin

aiwatarwa ba.

Ga Bidiyon

Matar ta bayyana dalilin da ya sanya aikata wannan

ɗanyen aikin

Matar mai siyar da zoɓon ta bayyana cewa:

“Naje asibiti wata shida da suka wuce inda aka gayamin

ina ɗauke da cutar ƙanjamau.”

“Na fara sanya jini na cikin zoɓon da nake yi na siyarwa

sannan na siyarwa da mutane da dama

“Na ɗebi jinina da sirinji sannan na haɗa shi da zoɓo.

Da ni ma’aikaciyar jinya ce amma bayan an tabbatar

ina ɗauke da cutar ƙanjamau dole na bar aikin.”

Matar ta bayyana dalilin da ya sanya aikata wannan

ɗanyen aikin

Ban ji daɗin abinda na aikata ba amma naji daɗi ba zan

mutu ni kaɗai ba.”

“Yanzu na kai wata shida ina yin wannan taɓargazar

sannan ina fatan ubangiji zai yafe min.”

Sai dai, binciken da jaridar The Punch tayi, ta gano cewa

ba’a ɗaukar cutar ƙanjamau ta hanyar ruwa ko abinci.

Comments

Popular posts from this blog