Tapswap code 14 July....

– Asiwaju Bola Tinubu ya karyata batun kara aurensa da
ya karade ko ina a yanar gizo, inda ya bayyana yadda suke
zaune lami lafiya gami da more rayuwar aurensu shi da
matarsa
– 'Dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, ya kara da
cewa, shi bai da niyyar dankaro wa matarsa kishiya, batu
ne kawai na masu son janyo rikici cikin iyalinsa
– Ya kara da cewa, burinsu ba zai taba cika ba, saboda
shi da matarsa a yanzu sun fi mayar da hankali kan
fafutukar yakin neman kuri'un don lashe zaben shugaban
kasa
'Dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola
Tinubu ya karyata "Wani labarin kanzon kurege" da ke yawo
a yanar gizo cewa zai kara aure, inda ya bayyana yadda
yake jindadin rayuwar aurensa da matarsa, Sanata Oluremi
Bola Tinubu ya Magantu Kan Rade-Rafin Kara Aure da Ake
Yadawa Zai yi. Hoto daga Vanguardngr.news
Mai magana da yawunsa, Tundra Rahman ne ya bayyana
hakan a wata takarda mai taken,:
"Ku Daina Yada Labarin Kanzon Kurege: Asiwaju Bola
Tinubu bai da niyyar kara aure.”
Takarda wacce ta fita daren Lahadi a Abuja .
"Mun ga labaran kanzon kuregen da ke yawo a yanar
gizo na cewa 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar
APC, Asiwaju Bola Tinubu zai kara aure.
"Wannan labarin kanzon kurege ne wanda bai da
tushe.
"Shi Asiwaju na morar aurensa da matarsa, Sanata
Oluremi Tinubu, wacce aka albarkata da 'ya'ya na
kwarai. Bai shirya kara aure ba, Musulma ko Kirista.”
- Kamar yadda takardar ta bayyana daga Ofishin yada
labaran Tinubu.
Kamar yadda takardar ta bayyana:
”Burin wadan da ke yada cewa zai auri musulma ba
kawai don su janyo rikici cikin iyalin Tinubu kadai bane,
sai don su jawo kiyayya tsakanin al'ummar kiristanci.
Shugaban Kasa: Duk Dan Takarar Da Wike Ya Marawa
Baya Ba Zai Ci Zabe Ba, Malamin Addini Ya Yi Gargadi
"Burinsu ba zai cika ba. Hakan ba zai yi tasiri ba."
Takardar ta roki 'yan Najeriya da su yi watsi da labarin
karyar.
"A halin yanzu, Asiwaju ya maida hankalinsa kan
kamfen don lashe zaben shugaban kasa da zai gudana
ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, ko ya dawo wa
jama'a buri, data da tsaro da farincikin Najeriya.
"Sanata Oluremi ita ma tana tsaka da fafutukar nemar
wa mijinta magoya baya. Hankalinsu bazai da
abaran kanzon kurege ba,"
Comments
Post a Comment