Yadda Mummunan Hatsarin Mota Ya Lashe Rayuka Da Dimbin Dukiya A Bauchi » Labarai


 Mummunan hatsarin mota ya ritsa da wasu bayin Allah

matafiya a garin Nabordo karamar hukumar Toro Jihar

Bauchi.

Wani wanda ya gane wa idon sa faruwan lamarin, ya

shaidawa ma wanema labarai cewa wata babban mota

kiran Tirela da wata Bamba sukayi aran gama . Sabila

da karfin buguwan nan take Motocin suka kama da

wuta.

Jama’a naji na gani babu halin isa gare su tun ana jin

motsi da ihun mutane har suka kone babu abinda

za’a iya musu sabila da karfin wutan da yake ci kuma

babu hukumar kashe Gobara a kusa .

See also Shani Jamilah Causes A Stir As She

Shares Gorgeous video – Yawadeyonline

Kwamandan yanki na hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa,

Yusuf Abdullahi, ya ce hatsarin ya faru ne a ƙauyen

Narbodo, karamar hukumar Toro.

Abdullahi, ya ce hatsarin ya ƙunshi motar bas ƙirar

Toyota Hiace da kuma babbar mota, wadda mutum uku

da ke cikinta ba su ji ko ƙwazane ba.

See also Ado Gwanja - Luwai Official Audio &

Video » Labarai

A cewarsa, lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4:40 na

yamma, kuma jami’an hukumar sun isa wurin cikin

minti bakwai da faruwarsa.

Kwamandan ya ɗora alhakin faruwan hatsarin kan

gudun wuce sa’a wanda ya haddasa motocin biyu

suka yi karo da juna.

Mutum 21 ne abin ya ritsa da su kuma akwai manya 18

da yara uku. !8 ɗin suna cikin bas ɗin kuma sun ƙone

ƙurmus bayan ta kama da wuta sakamakon karon da ta

yi da tirelar,” in ji shi.

Comments

Popular posts from this blog