Tapswap code 14 July....

Eeswar . Jarumi Prabhas Yasamu kyautar state Nandi Award for Best Actor , A Irin Rawar da ya Taka a Shirinsa na Mirchi. Baya Ga Haka kuma Jarumin Yayi Fitowa Ta Musamman a wata Wakar Shirin Bollywood Mai Suna ( Action Jackson ) da Mai Bada Umurni Prabhu Deva ke bada umurni keyi acikin Waka Mai Suna Punjabi Mast a shekara ta 2014 ,.
Prabhas ya kasance Jarumi na Farko a kudancin india da aka sassaka Mutun mutumin sa a aka ajiye shi a gidan tarihi na Madame Tussaud's wax museum .[5]
🧔🏻 Cikakken Sunan Shine Uppalapati Venkata Satyanarayana Prabha Raju, Anhaife shi a 23 ga watan October shekara ta 1979 , a yanzu haka Jaurimin nada Shekaru (40) a Duniya 🌎. An haifeshi a garin Madras.( Chennai) dake kudancin Kasar India .Kasar sa ta Haihuwa itace India🇮🇳
Ayukansa na Fina finai sun hada da: Varsham (2004), Chatrapathi (2005), Chakram (2005), Billa (2009), Darling (2010), Mr. Perfect (2011), da Mirchi (2013). Prabhas ya kafta rawa a shirin mai bada umurni S. S. Rajamouli Shirin Al'mara da kuma gumurzu mai suna Baahubali: The Beginning (2015), Baahubali 1 ya zamto shiri the fourth- highest-grossing Indian film to date. Prabhas ya sake kaftawa a cigaban Shirin sa mai Suna Baahubali 2: The Conclusion (2017), Wanda Shi Kuma Shirin ya zamto Shirin india na Farko da ya hada kudi kimananin ₹1,000 crore (US$155 million) a duka yarukan da aka sake shirin da duniya baki daya acikin kuma kwanaki Goma Kacal .Sannan kuma kuma shine shiri na biyu yake the
second highest-grossing Indian film a lokacin .
🙋🏻♂️Rayuwar shi daga Farko 👨🏻
Jarumi Prabhas Dane ga producer U. Suryanarayana Raju, mahaifiyar kuma itace Siva Kumari. Yanada yan uwa guda biyu , Dayan sunansa Prabodh da kuma yar uwarsa daya Sunanta Pragathi. Shine Karami acikin su ukun , Sannan Kuma Jarumin Telugu mai suna Uppalapati Krishnam Raju kawu ne a gareshi . Prabhas ya halarci Makarantar DNR School, Bhimavaram ya gama karatunsa a matakin B.Tech. degree a makarantar Sri Chaitanya College, dake Hyderabad .
🎬🎬Shigar sa Harkar Fina Finai 🎬🎬
Prabhas ya fara aiki a shirinsa na Farko mai suna Eeswar a 2002. a kuma 2003, ya jagoranci shirin Raghavendra. haka a 2004 ya fito a shirinsa mai suna Varsham . jarumin ya cigaba da kafta inda a gaba ya fito a shirin adavi Raamudu da kuma Chakram. a shekarar 2005 ya kafta a film din Chatrapathi wanda mai bada umurni S. S. Rajamouli ya bada umurninsa . Ida yafito a dan gudun hijira da yake gudu akan yan jagaliyar da aka bawa kwangila akansa. ya dauke shi kwanaki Dari yana guduwa acikin cibiyoyi 54. ya fito da salo na musamman kuma dan barazana hadi da siddibaru a yanda ya bayyana a shirin.
Bayan haka kuma ya fito a film din Pournami, Yogi da kuma Munna, sun zamto shirin action-drama da suka fita a shekarar 2007,
A biye dasu kuma ya fito a shirin Barkwanci da gwabzawa ( action-comedy) mai suna Bujjigadu a shekarar 2008. A 2009 kuwa ya fitarda film biyu da suka hada da Billa da kuma Ek Niranjan. Mujallar Indiaglitz ta bayyana shirin Billa amatsayin shiri mai Salo da kuma mai kudi na gani da ido.
A 2010 ya fito shirin soyayya da barkwanci mai suna Darling .Shirin ya samu sharhi mai kyau daga masharhanta. Mujallar The Times of India ta bawa Shirin Tauraro Biyu da Rabi ⭐⭐/*Yayinda sukayi Bayanin Director Karunakaran da irin kyakyan aikinshi daga kuma Jarumansa .
A Shekarar 2011 jarumin ya sake zuwa da shirin Mr. Perfect wanda shima ya kasance shine na Nau'in Soyayya . Masu sharhi na GreatAndhra sun bawa shirin da tauraro guda uku ⭐⭐⭐ sannan kuma suka bayyana cewa Shirin ya ya tsallake amatsayin tsaftatacce baya ga haka kuma yakasance Shirin Ahali ne mai nisha dantarwa sannan kudurin masu shirin ya zama dole a yaba musu.
A shekarar 2012, Prabhas ya fito a shirin Rebel , Film dinda yaka sance na Gumurzu film din yasamu damar bada umurni daga mai bada umurni Raghava Lawrence. Shirin sa na gaba kuma shine His Mirchi .Sashidhar daga Mujallar Times of India ya bayyana cewa , Shirin Ya Zamto Mallakin Masoyan Prabhas wadanda akoda yaushe suna tare dashi iya wuya amatsayin shirin nasa mai dauke da salo da kuma Bayya nanne mai kudi a shirin nasa.
"Mahesh S Koneru kuwa a bangaren nashi hukunci ya bayyana cewa , A Box Office Shirin zai taka rawa a bangaren kasuwancin sa dakyau sannan kuma ya bawa Shirin Ladan Tauraro ⭐⭐⭐"3.25/5. A bangaren Way2movies suma sun bawa shirin tauraro ⭐⭐⭐ 3.25/5, . Suma Super good movies sun bawa shirin taurari ⭐⭐⭐3 acikin ma'aunin 5, Bangaren Sharhinsu kuwa Sun bayyana cewa. " Tafi ka kalli Film din Mirchi ya nisha dantar kana ya kunshe komai duka biyun Aji da kuma Hadakar Al'umma kana Dajara ce Kallon sa.
A shekarar 2015 ya bayyana Amatsayin Shivudu/Mahendra Baahubali da kuma Amarendra Baahubali A shirin S.S. Rajamouli Na Al'mara mai suna Baahubali: The Beginning wanda yake matakin film na hudu acikin fina finan kasar india da suka tattaro kudade zuwa yanzu, Jarumi Prabhas ya cigaba Da Shirinsa Na Gaba Wanda Yake Cigaban Shirin Baahubali The Beginning ne wanda Shi Kuma Yake Baahubali 2: The Conclusion da ya fita a (2017), Inda Shi Kuma Shirin ya Zamto Shirin India na Farko Tilo da ya amsa Kudade Fiyeda ₹1,000 crore (US$155 million) A Duka Yarukan da aka Sake Shirin acikin Kwanaki Goma Kacal , Sannan Kuma shine shirin india na biyu da yafi amso kudade batareda ancire haraji ba a halin yanzu.
Fita ta Farko ta Poster film din Saaho an saketa ne A 23 Watan October shekarar 2017, a yayin kwankin bikin Murnar Zagayowar Haihuwar Jarumin, Haka Itama karamar Tallar Shirin nasa Fita ta biyu an sake tane a 23 ga October shekarar 2018 itama haka yayin Jajiburin Kwanakin Shagalin Murnar Zagayowar Ranar Haihuwar Jarumin.
Shirin sa Na Saaho ya kasance Shiri na Uku acikin Fina finanda ake dasu a India Mafi Tsada har zuwa yanzu.
Shirin da yake bai samu sharhi mai kyau ba daga masharhanta an masa Kasafi mafi yawa da ya kai ₹350 yayinda ya Amsa Kudade da Kimanin su yakai ₹130 a ranarsa ta farko a duk fadin duniya kamar yanda aka bayyana amma duk da hakan film din bai tsallake ga Faduwa ba, Yayinda acikin kwanaki Goma Shirin ya Amshi ₹400 crore (US$56 million) , yayinda shirin ya kare a matakin Mara Nasara 'Flop' ta Fuskar Kasuwanci a Box Office.
Shirinsa na gaba a halin yanzu Shine Radhe Shyam wande yake yana nan fitowa a shekarar 2021 shirin da yake na Launin Soyayyane wanda Rubutawar shirin da kuma Bada Umurnin sa sun rataya ne ga Radha Krishna Kumar , A shirin zamuga Jarumi Prabhas tareda Jaruma Pooja Hegde amatsayin Masu jagorantar Shirin .
Yayin Krishnam Raju ke gabatarda Shirin a karkashin Gopi Krishna Movies Sai wandanda suka dauki nauyin Shirin UV Creations da kuma T-Series .
🎬Director Shirin Radha Krishna Kumar.
🤵🏻Daukar Nauyi Vamsi Krishna Reddy
Pramod Uppalapati
Praseedha Uppalapati
Bhushan Kumar
✍🏻 Rubutawa Radha Krishna Kumar
⭐ Taurarin Shirin Sun Hada :
🤨Yaren Shirin , Telugu
🌟Prabhas
🌟Pooja Hegde
Cinematography, Manoj Paramahamsa.
A shekarar nan ne ta bayyana Jarumi Prabhas zaiyi aiki tareda Mai Bada Umurni Nag Ashwin wanda kamar yanda aka Bayyana Jarumin ya Saka hannu a Shirin yayinda zai fito tareda Jarumar Bollywood Deepika Padukone da zata jagoranci shirin itama, kamar yanda aka bayyana , bayaga haka an bayyana cewa Shiri da za ayiwa kasafi mai Tsoka .
Biyeda hakan acikin Wannan Shekarar Jarumin Ya sake Rattaba hannu a shirin Shudadde Karni a Labarin Gaske Wanda Director Daga Masana'antar Bollywood Mai Suna 'Om Raut' zai Shiryawa Jarumi shirin Mai Suna Adipurush shirin da ya ta allakane akan shudadden karni wanda yake labarin wani azzalumi da ya gabata Fiyeda Shekaru dari bakwai. .
.🚘 Wani Aikin Jarumin 🚘.
Jarumi Prabhas wanda ya saka hannu tuni amatsayin jakadan Kamfanin Motoci na Mahindra yayinda yasaka hannu amatsayin Jakadan Sabuwar motar Mahindra TUV300 car
Jarumi Prabhas ya shiga harkar kasuwanci ta Gidan Talebijin (TVC) a fagen tallata sabbabi abubuwa.
👉🏻👉🏻Jadawalin Fina Finansa👈🏻👈🏻
2002 Eeswar, ya Fito da Suna Eeswar
2003 Raghavendra,ya fito da suna Raghavendra.
2004 Varsham, ya fito da Suna Venkat.
2004 Adavi,ya fito da Suna Ramudu Ramudu
2005 Chakram, Ya Fito da Suna Chakram.
2005 Chatrapathi Siva / ya Fito da Suna Chatrapathi.
2006 Pournami ya Fito da Suna Siva Kesava.
2007 Yogi ya Fito da Sunaye Eeswar Prasad / Yogi.
2007 Munna , Ya Fito da SunaMunna.
2008 Bujjigadu, Ya Fito da Sunaye Bujji / Linga Raju / Rajinikanth .
2009 Billa , Ya Fito da Sunaye Billa / Ranga .
2009 Ek Niranjan, Ya Fito da Suna Chotu.
2010 Darling, Ya Fito da Sunayi Prabhas "Prabha".
2011 Mr. Perfect , ya fito da Suna Vicky.
2012 Rebel, ya fito da Sunaye Rishi / Rebel.
2012 Denikaina Ready yayi fitowa ta Musamman .
2013 Mirchi ya Fito da Suna Jai.
2014 Action Jackson, Yayi Fitowa Ta Musamman .
2015 Baahubali: The Beginningya Fito sa Sunaye Mahendra Baahubali / Shivudu / Shivu Amarendra Baahubali.
2017 Baahubali 2: The Conclusion , ya Fito da Sunaye Mahendra Baahubali, Shivudu.
2019 Saaho ya Fito da Sunaye Ashok Chakravarthy / Siddhant Nandan Saaho.
2021 Radhe Shyam tukunna ba'a bayyana ba.
2021 Adipurish , da sunan Adipurush.
Gambun yabo
2004 Varsham
Filmfare Award for Bes Telugu
Santosham Film Award Young Performer
2005 Chatrapathi Filmfare Award for Bes Telugu
2009 Ek Niranjan Filmfare Award for Bes Telugu
2010 Darling CineMaa award for Criti Actor
2011 Mr. Perfect
Filmfare Award for Bes Telugu
SIIMA Award for Best Telugu
2013 Mirchi
Nandi Award for Best
Filmfare Award for Bes Telugu
SIIMA Award for Best Telugu
2015 Baahubali: The Beginning
Filmfare Award for Bes Telugu
IIFA Utsavam for Best Telugu
IIFA Utsavam for Best Tamil
IBNLive Movie Awards
– South
SIIMA Award for Best Telugu
Santosham Best Actor
2017 Baahubali 2: The Conclusion
Filmfare Award for Bes Telugu
SIIMA Award for Best Telugu
2019 Saaho ETC Bollywood Business Highest Grossing.
Xuelqiflu Hassan BK.
Comments
Post a Comment