Tapswap code 14 July....

Shahrukhan ya kasance maraya ne .............................
Amma ga cikakken tarihin
Tarihin Shahrukhan Kashi Na 1.
An Haifeshi 2 Ga Watan Nuwamba 1965 Wanda Aka Fi Sani Da SRK Ana Mai Laqabi Da "Badshaah Of Bollywood" Ma'ana (Sarkin Bollywood).An Haifeshi A Cikin Musulunci A Garin New Delhi Inda Ya Tashi A Hannun Kakansa Ifthikar Ahmad Wanda Chief Engineer Ne A Tashar Jirgin Kasa A Daidai Shekarar 1960.
Sunajin Yaran Hindko Inda Aka Tabbatar Asalinsu Daga Kashmir Suke Bayan An Raba India.Sunan Mahaifinsa Mir Taj Muhammad Mahaifiyarsa Kuma Lateef Fatima Wanda Sunyi Aure A Shekarar 1948. Ya Taso A Yankin Rajendra Nagar Inda Yake Maqontaka Da Yankin Dhelhi, Mahaifinsa Karamin Dan Kasuwa Ne Wanda Yana Da Wajen Cin Abinci Inda Suke Zaune A Dan Karamin Gidan Haya A Wannan Lokacin.
Yaje Makarantar St Columbas School A Delhi Inda Ya Kasance Dalibi Me Kwazo Sosai Wanda Ba A Iya Karatu Ba Har Wasanni Ba aBar Shi A Bayaba Inda Yana Buga wasan Cricket Da Kwallon Kafa Amma Daga Baya Ya Jingine Harkar Wasanni Sakamakon Rauni Da Ya Samu A Kafadar Sa Inda A Lokacin Yana Dan Fitowa A Wasanni Da Suka Danganci Na Kwaikwayo Da Dai Sauransu, Yanayin Actin Nasa Yana Ake Kwaikwayon Wasu Jarumai Na Bollywood A Wannan Lokacin Inda Yace Wadanda Ke Burgeshi Sune Dilip Kumar, Amitabh Bacchan Da Mumtaz. Daya Daga Cikin Abokansa A Wannan Lokacin Itace Amrita Singh Wadda Itama Ta Zama Jaruma A Bollywood.
Yayi Karatun Digirinsa Na Farko A Makarantar Hansraj College Daga 1985 Zuwa 1988 Inda Daganan Ya Wuce Digirinsa Na Biyu A Jamia Millia Islamia Inda Bai Karasa Ba Ya Jingine Ya Kama Harkar Film.Mahaifinsa Ya Rasu Sakamakon Cancer Da Yayi Fama Da Ita A Shekarar 1981 Inda Mahaifiyarsa Ta Mutu A 1991 Sakamakon Cutar Diabetes.
Ya Auri Gauri Chiber (Gauri Khan) A 25 Ga Octoba 1991 A Daurin Auren Da Akai Bisa Tsarin Addini Da Al'adar Hindu Wadda Sun Haifi Yaya Uku Wadda Suka Hada Da Aryan 1997, Suhana 2000 Sai Abram 2013 Wanda Aka Sameshi Ta Hanyar Surrogacy.
Kash Mu Hadu A Kashi Na Biyu Danjin Yadda Akai Shahrukhan Ya Shiga Film Da Kuma Qalubalen Daya Fuskanta.
Ku Huta Lafiya
Comments
Post a Comment