Tapswap code 14 July....
Wata jaha ce a america da aka bani award kuma sai aka
yi wani film mai suna Naburaska, film din zai kai shekaru
17 ko 18.
YAUSHE KA FARA FILM?
Na fara sana’ar film a 2001 zuwa 2002.
DA WANI FILM KA FARA?
Bazan iya tunawa ba.
KAI DAN ASALIN WANI STATE?
Ni dan jihar kano ne.
ZAMU IYA SANIN ASALIN SUNANKA?
Shekaruna 35.
KANA DA MATA NAWA?
Ina da mata biyu.
SHIN KANA SON KA KARA WATA MATAR?
Eh ina da niyar yin hakan. Ina son na auri Hadiza Kabara.
YAUSHE ZAKU YI AUREN?
Sai lokacin da Allah ya ƙaddara.
KAI KAKE ZABAR YIN BARKWANCI A FINA-FINAI?
Bani nake zaba ba, kawai idan an ga na dace sai a saka
ni.
AN TABA DUKAN KA DA GASKE A FILM?
Eh, an taba yi min dukan gaske a film sau da yawa.
WA KA TABA DUKA A FILM?
Na taba dukan Tijjani Asase a film kuma yayi min korafin
yaji zafi kuma idan an hada mu a wani film zai rama shi
ma.
YA KAKE JIN YADDA MUTANE KE MAGANA GAME DA
‘YAN MASANA’ANTAR KANNYWOOD?
Ai mutane suna kallon mu, yanayin shigar mu da yanayin
mu’amalar mu, bai sai mutum ya wahala wajen
bayyana shi mutumin banza ba, duniya ce zata bayyana
kai mutumin banza ne, idan kuma ka zama mutumin kirki
ba sai ka wahala ba, duniya zata bayyana ka. Abinda na
sani shi ne majority din yan film ‘ya’yan malamai ne,
ciki har da ni, duk abinda zai taba addini na da Al’ada
ta ina kauce masa, sannan bazan iya yin abinda zai taba
mutuncin iyalan mu ba.
KA CE MAHAIFINKA MALAMI NE KUMA KAI KUMA
ALMAJIRI NE, IZUNKA NAWA?
Nasan abubuwa da yawa a cikin Alkur’ani daidai
gwargwado.
BAYAN FILM AKWAI WATA SANA’A DA KAKE YI?
Ni dan kasuwa ne bayan kasuwancin Film kuma dan
siyasa ne ni.
A WANI FILM NE KASHA WAHALA SOSAI?
Film din da nasha wahala sosai a cikin sa shi ne film din
Basaja.
ME YA BA KA WAHALA A FILM ƊIN BASAJA?
Su na da yawa domin akwai wuraren da murya nake
canjawa, wani wuri zan yi muryar maza wani wuri zan yi
muryar mata, wani wurin kuma muryar malamai nake yi.
A FILM DIN GIDAN BADAMASI WACE CHARACTER CE
TAFI BIRGE KA?
Character da yafi birgeni a gidan badamasi, shi ne
character da nayi.
TA YA KAKE CANJA SALON MAGANA ZUWA TA ‘YAN
DABA?
Yadda Mustapha yake canja muryar sa ko kuma yadda
bazuka yake canja muryar sa, shine yanzu kana ji na
canja murya ta ya koma irin ta ‘yan daba.
SU WAYE MANYAN ABOKAN KA 3 A KANNYWOOD?
Idan kace abokai 3 sun yi kadan, domin duk wanda yake
da alaka da comedy abokina ne, producers, directers
duka abokaina ne.
KA FADA MANA ABINDA IDAN KA TUNA SAI YA BAKA
DARIYA?
Abinda idan na tuna yake bani dariya shi ne. Wani
mugunta da na taba yi wa Bosho a lokacin da muke
shooting, na diɓo kudade da yawa na zuba a gabansa
kusa da wani bafulatani nace ga kudin aikin ka, sai
hankalin shi ya tashi ya fara zage-zage yana cewa “ni
za’a tonawa asiri” to wannan abin ya ban dariya sosai.
KA IYA WAKA?
Ban iya waka ba.
AMMA A SERIES DIN GIDAN BADAMARI AN GANKA
KANA WAKA?
Tabbas a Gidan badamasi na rera waka da jita, amma
director shi yake fada min abinda zan fada a wakar.
WANENEN GONINKA A GIDAN BADAMASI?
Kwani na a film din gidan badamasi shine dankwambo.
ME YASA DAKWAMBO YA ZAMA GWANINKA?
Allah yajikan Rabilu musa dan-ibro idan yana acting yana
min kama da shi.
KA FADA MANA BURIKA 3 DA KAKE SO KA CIMMA
ANAN GAB?
Burika 3 da nake so na cimma a rayuwata ta duniya bai
wuce kan sana’a ta ba, na farko gwamnati ta tallafa
mana kamar yadda muke tallafa ma ta, na biyu mu sami
kyakkyawar tsari a masana’antar mu ta kannywood
sannan mu samu kyakkyawar shugabanci, wa’yannan
su ne manyan burika na a duniya.
ME YAKE SAURIN BATA
Ganin Almajirai akan titi, wannan yana bata min rai sosai.
GODIYA MUKE GAREKA?
Muma haka.
Comments
Post a Comment