Tapswap code 14 July....

Littafi na daya 1
Na Abdulaziz sani m gini
Typing:- yusuff smært
Part 1📌
_____________________
.
marubucin littafin yace
Saurayin gudu yake iya karfinsa acikin dajin
domin ya
ceci rayuwarsa,
.
yana gudu yana waigen bayansa cikin
tsananin tsoro,amma baya ganin komai kuma
baya
jin sautin komai face na masifaffun karnukan
dake
biye dashi.
.
Su dai wadan nan karnuka sun kai guda saba in
da
doriya kuma sun kasance jibga jibga tamkar ba
karnuka bane kai kace kurayene sabo da
girmansu da
kwarjininsu gami da ban tsoro,musamman aka
kiwata wadan nan karnukan kuma aka basu horo
na
musamman domin suyi gadin babban kurkuku na
birnin Kisra.
.
A tarihin birnin na kisra tunda aka gina kurkukun
tsawon shekaru arba in ba ataba samun fursuna
da
ya taba guduwa daga cikin sa ba sabo da karfin
tsaron da ke cikinsa sai wannan saurayi wanda
ake
kira IMHAL IBN IMZANU,
.
sabo da tsananin karfin
gudun Imhal ne ya baiwa karnukan tazara ta
kimanin
taku sittin amma sabo da nacin karnukan da
mugun
horon da suka samu sai gashi sun fara hango
shi,nan
fa suka kara kaimi,nan fa Imhal ya kara kaimin
gudunsa alokacin da ya waigo ya hango su yaci
gaba
da falfala azababben gudu ta cikin kwazazzabai
da
sarkakiya,
sabo da karfin gudun ma har tashi sama
yake yana tsallake duwatsu da karyayyun
bishiyoyin
da suka fadi kasa
.
Shi dai Imhal gudun kawai yake yi acikin dajin
amma
baisan inda yake dosa ba,sabo da baisan ma a
inda
yake ba bare ma yasan hanyar da ya kamata
yabi, a
duk sanda ya tuno da bakar wahalar da ya sha
kafin
ya sami nasarar guduwa daga kurkukun sai ya
kara
kaimin gudun nasa yana mai ayyanawa a ransa
da dai
a kamasa a raye a mai dashi cikin kurkukun
gwara a
sami gawarsa sabo da azabar da take cikin
kurkukun
ta wuce tunanin mai tunani.
.
Asalin Imhal bin Imzanu mutumin birnin misira ne
kuma shi ba dan kowa bane kuma bai aikata
laifin
komai ba,mahaifinsa wani makiyayi ne mai kiwon
dabbobi a daji,don haka rayuwar Imhal gaba daya
a
cikin daji take,sai dai a karshen kowane sati
ranar
Lahadi sukan shiga cikin gari suyi dan siye-siyen
su
sannan su koma daji inda suka gina bukkarsu.
.
Imhal ya taso da Jarumtaka juriya da iya
farauta,sanan komai yawan dabbobi idan ya tafi
kiwo
dasu yana iya sarrafa su
.
Lokacin da Imhal ya fara girma ya cika shekaru
goma
sha shida ne ya tambayi mahaifinsa tsoho
Imzanu
yace ya kai Abbana me yasa baka taba bani
labarin
mahaifiyata ba?ban santa ba kuma bansan yanda
akayi ta mutu ba kullum sai kace dani kawai
mutuwa
tayi,kayi sani cewa yanzu ni ba yaro bane karami
na
mallaki hankalin kaina yakamata ka sanar dani
gaskiyar al amari,
koda tsoho Imzanu yaji wannan
batu sai hankalinsa ya dugunzuma ainun yayi
shiru
yana mai sunkui da kansa kasa,kawai sai
idanunsa
suka ciko da kwalla hawaye ya fara zubowa kas,
a sannan ne ya dago kai ya dubi Imhal yace
yakai dana
kasani yau ka tambayeni wani sirri wanda dama
nayi
alkawarin bazan sanar dakai ba sai bayan ka
mallaki
hankalinka,don kada hankalinka ya dugunzuma
kwakwalwarka ta kasa daukar al amarin, koda
imzanu
yazo nan a zancensa sai ya sake yin shiru kamar
bazai
iya cewa komai ba,da kyar ya sake dago kai ya
dubi
Imhal muryarsa na rawa yace ka gafarceni yakai
dana
bisa abinda zaka ji daga bakina yanzu domin
zakayi
matukar mamaki kuma zai iya girgiza
ka,maganar
gaskiya ita ce ni ba mahaifinka bane na jini,koda
jin
wannan batu sai zuciyar Imhal ta buga da
karfi,nan
take idanunsa suka kada sukayi jawur,bai san
sanda
hawaye ya zubo masa ba yace yanzu idan ba
kaine
mahifina ba to wanene? Bansan kowa ba a
rayuwata
sai dai kai kadai,
kaine kasan cina da shana tundaga
kuruciyata har izuwa yanzu,me yasa uban nawa
ya
gujeni ya barni a wajanka cikin daji inda babu jin
dadi da tsaro?
.
lallai kuwa ashe babu soyayya tsakani
na da uban nawa tunda bai damu da rayuwata
ba.
Koda Imhal yazo nan a zancensa sai tsoho
imzanu ya zubar
da hawaye sannan yace
Ni kaina bansan waye
mahaifinka ba,ka saurara dakyau kaji labarin da
zan
baka yanzu,
wata kila idan kaji labarin zuciyarka tayi
sanyi ka rungumi kaddara a bisa halin da ka
tsinci
kanka a ciki
....... ..¤¤¤¤¤¤¤
Wata rana da safe na fito kiwo acikin dajin nan
ina
kada dabbobi na sai kawai na hango wasu
mutane
bisa keken doki sanye da bakaken tufafi kuma
sun
rufe fuskokinsu su biyu sun nufi bakin wani katon
rami mai zurfi da fadin gaske,cikin hanzari na
kada
dabbobina izuwa cikin duhuwar bishiyoyi nima na
sami wuri na buya,
dama wadannan mutane basu
ganni ba,ina nan labe cikin duhuwa sai naga
wadannan mutane sun fiddo gawar wata mace
daga
cikin keken dokin sun cillata cikin wannan
ramin,
kawai sai suka shiga cikin keken dokinsu da
sauri suka fice daga cikin dajin gaba daya,sai da
na
tabbatar da cewa sunyi nisa da tafiya kuma babu
alamar cewa zasu dawo sannan na ruga izuwa
bakin
wannan ramin na leka cikinsa kawai sai naga
ashe
wata kyakkyawar mace ce aka yanka ta har a
sannan
jini na bulbulowa daga cikin makogwaronta kuma
tana dauke da tsohon juna biyu,nan take naji na
kamu da tsananin tausayinta,
.
don haka sai na yanke
shawarar na shiga cikin ramin na dauko gawar
wannan mata domin na suturta ta sosai na haka
kabari mai kyau na binne ta,idan ma na barta
acikin
ramin zata rube ne warinta ya dameni tunda
ramin
yana kusa da inda bukkata take,nan fa na fara
tunanin
dabarar da zanyi na iya shiga cikin wanna har
na iya dauko gawar,sai da nayi tunani na tsawon
'yan
dakiku sannan dabara ta fado mini,kawai sai na
ruga
da gudu izuwa cikin bukkata,na dauko igiya mai
tsawo
sannan na dawo bakin ramin,na daura igiyar a
jikin
wata bishiya na wurgata cikin ramin sannan na
kama
igiyar ina binta ina shiga ramin,sannu a hankali
na isa
kasan ramin,koda naje kan gawar na duba ta sai
naga
ashe da ranta bata mutu ba domin numfashinta
na
fita kadan-kadan,cikin gaggawa na sunkuci
wannan
mace na goya ta a bayana na daureta tamau,na
sake
kama igiyar nayi iya kokarina na fito daga cikin
ramin
goye da matar a baya na,hankalina a
dugunzume,sauri nake kawai na jarraba ceto
rayuwarta,ina fita daga cikin ramin na ruga da ita
izuwa cikin bukkata,na shimfide ta a kasa
sannan nayi
sauri na dauko allura da zarin dinke fata na dinke
raunin wuyanta sannan na shafa magani akan
raunin,A sannan ne na kara hancina a dai dai
hancin
matar don naji ko tana yin numfashi,amma sai
naji
shiru alamar babu rai a jikinta,nan fa bakin ciki
ya
lullube ni naji kamar na fashe da kuka sabo da
takaici,gashi nasaa wahalar dauko ta daga cikin
wannan ramin mai zurfi har ma tafin hannuwana
sun
dade saboda kama igiya,cikin sanyin jiki na mike
na
sunkuya da nufin gawar na fita da ita waje
inda zan binne ta,kawai sai naji tayi
tari,numfashint
a
ya dawo,nan take murna ta kamani na ruga na
dauko
wani ruwan magani na dura mata a baki dakyar
tasha
mukurwa uku,jin kadan sai idanunta suka bude
dakyar,koda tayi arba dani sai naga ta firgita ta
yunkura zata tashi amma sai na danne kafadunta
na
hana ta tashi,matar ta budi baki da nufin tayi
magana
sai ta kasa,kawai sai naga tana dariya,wani
lokacin
kuma sai ta hade fuska ta kama kuka tana fisge-
fisge,nan fa na gane lallai wannan mata ta samu
tabin
hankali,al'amarin da yayi matukar bakanta raina
kenan domin naso ace ta iya yin magana acikin
hankalinta,domin na tambayeta ko ita wacece da
kuma wadannan mutane da suka kawo ta dajin
acikin
keken doki a matsayin gawa,abinda zuciyata ta
aiyana
min shine in ma basu bane to sun san wanda ya
kasheta,kuma akwai wani boyayyen al'amari akan
kisan nata,daga wannan rana naci gaba da jinyar
wannan mata har tsawon kwana ashirin da
daya,A
tsawon wadannan kwanaki kullum a kwance take
kuma koda tayi yunkurin mikewa zaune sai ta
kasa
sabo da raunin da yake makogwaronta,haka
kuma
bata taba yin magana ba sai fisge-fisge da dariya
irinta mahaukata,abinci kuwa sai dai na dura
mata
abaki tana ci tana kuka sabo da ciwo,da yake
naga
tana dauke da juna biyu sai na dinga yawan bata
madarar shanu gami da abincin da yake gina jiki
domin abinda ke cikinta ya samu cikakkiyar
lafiya,a
kwana a tashi har wannan mata ta shafe wata
uku cur
a wajena,a sannan ne raunin makogwaronta ya
warke sumul har ya zamana cewa tana iya
magana
sosai,amma a koda yaushe babu magana ta
hankali
da nutsuwa a tare da ita sai maganganu irin na
mahaukata,nayi iya kokarina akan ta gayamin ko
ita
wacece,daga inda take da kuma yadda akayi ta
shiga
wannan hali sai tayi ta kyalkyala mini
dariya,ganin
hakane yasa tausayinta ya karu a zuciyata,sau
bakwai
ina nemo masana ilimin maganin
mahaukata,wato
likitocin mahaukata suna zuwa su dubata kuma
su
bata magani,amma duk a banza lafiya taki
samuwa,sau tari matar takan sulale ta nausa
cikin
daji bansani ba,sai nasha wahalar nemota,bisa
wannan dalilin ne ma duk sanda zan fita kiwo ko
farauta sai na tafi tare da ita,wato na daina
barinta a
gida.
Lokacin da cikinta ya tsufa sai tafiya da ita kiwo
ko
farauta ya gagara,don haka nima sai na hakura
da
zuwa ko ina,na tanadi abincina da na dabbobi na
mai
yawa wanda zai kai tsawon kwana arba in,Ai
kuwa
adaren kwana lo talatin da bakwai nakuda ta
kama
wannan mata acikin tsakiyar dare.Al'amarin da
yai
matukar dugunzuma hankalina kenan tunda babu
halin in ruga cikin gari in nemo ungozoma,Da
yake na
taba shiga irin wannan hali da nake tare da
matata
wacce ta rasu a wajen haihuwa abinda ta haifa
ma
yazo a mace,sai na shiga taimakon wannan
mata,nine
na yankewa jaririn cibiya,na wanke shi sannan na
kimtsa mahaifiyar tasa,matar taci gaba da rainon
jaririnta tana shayar dashi ni kuma ina cigaba da
fita
farauta da kiwona ina barinsu a gida,har tsawon
shekara daya da wata bakwai muna tare sannan
yaron ya fara tafiya da kafafunsa.
Kwatsam wata rana naje kiwo na dawo sai na
nemi
wannan mata sama da kasa na rasa,kuma ga
dannan
ta bar shi acikin bukka a zaune shi kadai yana ta
tsala
kuka,cikin dimaucewa na dauki yaron na gaya shi
a
bayana sannan na bazama neman wannan mata
wacce ko sunanta ban saniba bare na dinga
kwalla
mata kira,Abu kamar wasa sai da na shekara
daya da
wata tara ina nemanta amma ko alamunta ban
gani
ba acikin wannan daji.A tsawon wannan lokacin
ni
nake kula da wannan yaro da ta haifa dare da
rana,ya
zama cewa na shaku dashi ainun shima haka
.Kwatsam wata rana da yammaci ina wasa da
yaron a
kofar bukkata kawai sai na hango wannan mata
daga
can nesa ta durfafo bukkata,cikin alamun
tsananin
mamaki na mike tsaye na zuba mata idanu,matar
ta
rame matuka,kuma duk rigar jikinta ta
yayyage,sannan tayi baki sabo da wahala da
kazanta,koda ta iso daf dani ta dubeni sai ta
fashe da
kuka ta durkusa kasa bisa gwiwoyinta tana mai
neman gafarata tamkar mai cikakken hankali,nan
take
naji na kamu da tsananin tausayinta don haka sai
na
kama kafadunta na tasheta tsaye kuma na
rungumeta
a kirjina a karon farko tun haduwa ta da ita,ita
kuma
sai ta kankame ni ta da da fashewa da
kuka,kawai sai
na janye jikina daga nata na dubeta nace me
yasa
kika gudu kika barmu?shin kin manta ne cewa
kin bar
danki a hannu na?koda jin haka sai matar ta dubi
dan
nata ta girgiza kai tace ai ni kananin yaro na bar
maka
bai kai wanan girma ba,da jin haka sai nayi
dariya
nace to ai kullum mutum dada girma yake har
yanzu
baki gaya min inda kika tafi ba kika barmu,Matar
ta
bushe da dariya sannan ta hade fuska tace shan
iska
na tafi na sake dawowa.Cikin tsananin damuwa
nace
yau shekara hudu kenan muna tare baki taba
gaya
min sunanki ba kuma baki gaya min sunan
garinku ba
bare nasan asalinki da danginki shin bakya
tausayin
wannan yaron da kika haifa ne?Koda jin wannan
tambaya sai matar ta sake bushewa da dariya
tace
bansan kaina ba kuma bansan kowa ba sai
kai,tana
gama fadin haka ta juya ta shige cikin bukka taje
ta
kwanta ta kama bacci,tun daga wannan rana
muka ci
gaba da zama tare,amma ko kadan wannan da
nata
bai dameta ba,kuma bata yi masa komai sai dai
ni
nayi masa,wani lokaci sai naga kamar hankalinta
ya
dawo tana magana a nutse,amma da zarar na
fara
tambayarta asalinta da garinsu sai ta birkice ta
koma
hauka.
Wata biyu da kwana uku mukayi tare ranar
kwana na
ukun ne matar ta wayi gari da tsananin rashin
lafiya
wadda bansan sanadinta ba,cikin rudewa na
shiga
hada mata magunguna iri-iri ina bata tana sha
amma
duk a banza tamkar kara mata ciwon akeyi,kawai
sai
naga idanunta sun fara lumshewa kuma
numfashinta
na sarkewa,Al amarin da ya dugunzuma
hankalina
kenan na fara zubar da hawaye,na shiga yi mata
tambayoyi akan ta sanar dani asalinta,matar na
kokarin bude baki tayi magana amma sai ta
kasa,nan
take jikinta ya sandare,idanunta suka kafe ta
daina
motsi.koda naga haka sai na rungumeta na fara
kuka,ganin ina kuka ne dannata wannan yaro dan
shekara kusan hudu ya rugo izuwa kaina shima
ya
fashe da kuka.Hakika wanan rana nayi kuka mai
yawa
sabo da shakuwar da nayi da matar nan sai da
nayi
kwana ashirin da daya bana iya cin abinci
sosai,amma koda yaushe hankalina yana kan
wannan
yaron ina kula da lafiyarsa sosai.
Koda tsoho Imzanu yazo nan a zancensa sai
Imhal ya
tari numfashinsa suka dubi juna a lokacin da
kowannensu yake zubar da hawaye yace yakai
Abbana na gane cewa wannan yaro da
mahaukaciya
ta haifa ba wani bane face ni dinnan,tabbas
yanzu na
tabbatar da cewa ni marayane wanda bashi da
uwa
bashi da uba kuma wanda baisan asalinsa
ba,koda
Imhal yazo nan zancensa sai tsoho Imzanu ya
rungumesa suka fashe da kuka tare,can sai
Imhal ya
janye jikinsa suka fuskanci juna ya dubi Imzanu
yace
Bazan taba yarda bani d uba ba amma ni kai na
sani
a matsayin ubana,ina son nayi maka wata
tambaya
guda daya menene dalilin da yasa kake kirana da
suna IMHAL?
.
WASA FARIN GIRKI
____ shin acigaba ko Kuma?
Comments
Post a Comment