Tapswap code 14 July....
littafi na daya
Part 2
By Yusuff smart
________
Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa
tsoho Imzanu yace Abinda yasa nasa maka suna
Imhal shine a iya zama na da mahaifiyarka har ta
mutu ban taba jin ta ambaci sunan wani mahaluki ba
face IMHAL,A kullum duk sanda za taci abinci sai naji
tana kiran sunansa tana cewa yazo suci abincin
tare,abinda na fahimta shine,koma wanene wannan
Imhal din lallai ya kasance babban masoyi a
gareta,zai iya kasancewa mijinta ne ko dan uwanta ne
ko mahaifinta,Abu na biyu da nake zargi shine,duk
yadda akayi mahaifiyarka ta fito daga babban gida
domin a ranar da na tsince ta acikin wannan katon
ramin mai zurfi sutturar dake jikinta mai matukar
tsada ce,babu mai sanya irinta face sarakai da
manyan attajirai,babban bakin cikina shine babu
wata shaida a tare da mahaifiyarka wadda zata iya
sawa a gano asalinta,koda tsoho Imzanu yazo nan a
zancensa sai suka sake rungume juna,daga can sai
Imhal ya dubi tsoho Imzanu yace,Lallai zan rike
sunana a zuciyata da bakina,lallai wata rana wannan
suna zai taimakeni na gano asalina.
Tun daga wannan rana Imhal da tsoho Imzanu suka
cigaba da rayuwarsu acikin daji kamar yadda suka
saba,amma sai ya zamana cewa kullum sai Imhal ya
shiga cikin garin Kisra kuma duk inda yaje si ya
tambayi mai suna Imhal,idan aka tambayeshi wane
Imhal yake nema sai ya kasa bayani domin baisan
wata inkiya ba ta Imhal din da yake nema,hakane
yasa suka dinga yiwa Imhal dariya suna cewa dashi
Bagidaje mutumin daji,saboda ganin yanayin
shigarsa ta makiyaya.
Wata rana Imhal yazo giftawa ta kofar gidan sarkin
kisra akayi sa a kuwa a lokacin sarki ya fito daga cikin
gidan sarautar zai fita rangadi kwatsam sai yayi arba
da sarki,Abinka da wanda baisan yadda ka idar
sarauta take ba sai kawai ya kurawa sarki
idanu,maimakon ya zube kasa gabansa ya kwashi
gaisuwa,ai kuwa sai dakarun sarki suka afkawa Imhal
da duka har suka kai shi kasa,cikin fushi ya yunkura
ya watsar dasu duka duk da cewar sunkai su
ashirin,nan take shima ya rufesu da duka,duk wanda
yayi wa naushi daya sai ya baje a kasa
sumamme,koda ganin haka sai ragowar dakarun
sarki suka zare takubbansu sukayi caa akan Imhal
zasu sassara shi,amma sai sarki ya daka musu tsawa
suka saurara,nan take sarkin kisra ya sauko daga kan
dokinsa yazo daf da Imhal yadda har suna iya jin
numfashin juna,sannan ya dubeshi cikin murmushi
yace,A duniya babu abinda yake birgeni sama da
jarumtaka,tabbas na yarda kai jarumi ne amma ina
son na gwada jarumtaka ta akan taka,nasan baka san
koni waye ba to nine Sarkin garin nan,koda jin haka
sai Imhal ya zube kasa bisa gwiwoyinsa yana mai
sunkui da kansa kasa yace ka gafarceni ya
shugabana,kasan cewa ni rayuwata gaba daya cikin
daji nayi ta,sau daya a sati muke shigowa cikin
garinnan,yau ne ranar farko da na fara ganinka a
rayuwata,ya shugabana kayi min afuwa domin bazan
iya fada da kai ba,Koda jin wannan batun sai sarki ya
bushe da dariya ,lokaci guda kuma ya hade rai ya
dubi Imhal cikin nutsuwa yace,ya kai wannan saurayi
ma abocin jarumtaka kayi sani cewa nahiyar nan
gaba daya babu wani jarumi ko mayaki mai karfi da
iya yaki kamata,yau shekara talatin kenan ina
gwagwarmaya da gumurzu kuma sau arba in da uku
ina lashe GASAR JARUMTAKA a kasashe arba in da
uku dake cikin wannan nahiya tamu ko sau daya ba a
taba samun jarumin da ya lakuci jikina ba bare ya
kaini kasa,naga jarumtakar jarumai da yawa a
rayuwata,amma ban taba ganin jarumi mai zafin
nama da karfin naushi kamarka ba,ina da tabbacin
cewa idan muka fafata sai na sami nasara akan ka
duk da cewar na yaba da karfinka,ka sani cewa kana
da zabi guda biyu kodai ka yakeni ko kuma yanzun
nan nasa tagobi na sare maka kai,koda jin wannan
batu sai hankalin Imhal ya dugunzuma ya mike tsaye
cikin sanyin jiki,abu na farko da ya fado masa a rai
shine,Ai bai kamata ya mutu yanzu ba har sai ya gano
asalinsa,koda gama aiyana hakan acikin zuciyarsa sai
ya mikawa wani badakare hannu yace bani
tagobinka,ba tare da gardama ba kuwa ya mikawa
Imhal tagobinsa ya karba,koda ganin haka sai murna
ta kama sarki,shima ya zare tagobinsa,a lokacinne
dakaru suka buda suka yi musu da ira aka sa su a
tsakiya,nan fa sarki da Imhal suka fara zagaya juna
suna kallo-kallo.
Lokaci guda kowannensu ya daga tagobinsa sama
suka ruga izuwa kan juna,suka ruguntsume da
azababben yaki ya zamana suna kaiwa juna sara da
suka cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta ta
ban al'ajabi,sai da suka shafe sa a guda suna wannan
bakin artabun amma dayansu bai samu nasarar koda
kwarzanar mutum daya ba,Al'amarin da ya fusata
sarki kenan kuma ya cika da tsananin mamakin yadda
akayi wannan mutumin dajin ya samu gagarumin
horon yaki haka,nan take sarki ya canza salon yaki,ya
dinga tsalle-tsalle da kwance-kwance,kawai sai yaga
Imhal ya iya duk irin abinda yake yi tamkar tare aka
koya musu yaki babu wani banbanci,koda ganin haka
sai sarki ya ja da baya taku biyar,shima Imhal sai yayi
hakan amma shi taku uku yayi,duk su biyun suka
kurawa juna idanu na tsawon yan dakiku kadan,kawai
sai sarki ya rugo da gudu izuwa kansa,shima sai ya
ruga gareshi,kafin su hadu sai kowannensu ya daka
wawan tsalle sama ya kai hari cikin mugun nufi,Acikin
tsananin zafin nama kowannensu ya kaucewa harin
takubbansu suka sari iska,amma kafin su duro kasa
sun gwarawa juna fuska,ai kuwa sai hancin
kowannensu ya fashe,a saman sai suka sake kaiwa
juna hari,sai sarki ya sami nasarar yankar Imhal a
saman cibiyarsa,Shi kuma ya sami nasarar yankar
sarki a gefen wuyansa,kowannensu jini yayi tsartuwa
daga jikinsa suka rikito kasa a matukar galabaice,A
guje Dakaru suka ruga aka baiwa Sarki rawani ya
daure wuyansa da jini,take likitan Sarki yayi masa
magani,Kawai sai Dakaru suka ruga izuwa kan Imhal
wanda yake kwance a kasa ya dafe raunin don tsaida
jini zasu halaka shi,Sarki ya daka musu tsawa suka
fasa,kawai sai sarki ya dubi likitansa yace Idan ka
gama dani kaje kayiwa wannan saurayin magani,Cikin
gaggawa kuwa likita ya gama yiwa sarki magani
sannan yaje yayiwa Imhal,Sa ar da Sarki da Imhal
sukayi raunikan basuyi zurfi ba a jikin su,Tunda
Likitan ya fara yiwa sarki magani sai zuciyar Sarki ta
fara tafarfasa kamar zata kone saboda tsananin bakin
ciki da takaici bisa ganin yadda a yau wannan bakon
saurayi ya karya alkadarinsa na jarumin dake rike da
KAMBUN JARUMTAKA na nahiyar gaba daya,Bayan
angama yiwa Imhal magani ya mike tsaye sai yazo
gaban Sarki ya risina yayi godiya,Sarki ya dube shi
cikin yake yace Tabbas ka cika jarumi abin kwatance
amma ka saurari ranar da zamu sake haduwa a filin
gasar JARUMTAKA wacce za ayi a birnin MISIRA nan
da cikar wata uku,ko kana so ko baka so sai ka shiga
wannan gasa kuma ina tabbatar maka da cewar sai
na sami nasara akan ka na kasheka murus har
Lahira,yin hakane kadai zai sa na huce bisa takaici da
bakin cikin da ka jefani a ciki,Koda ya gama fadin
hakan sai Sarkin Kisra ya dubi wani babban Badakare
nasa yayi masa rada a kunne sannan ya juya ya kama
dokinsa ya hau ya kada linzaminsa yayi gaba,sauran
dakarun gaba daya suka rufa masa baya.Shi kuwa
jarumi Imhal sai ya tsaya cak yabi sarkin kisra da
kallo cikin tsananin mamaki,Imhal ya tambayi kansa
cikin zuciyarsa yace WAI SHIN MENENE YAYI ZAFI
HAKA,HAR DA SARKI YACE ZAI KASHENI MURUS HAR
LAHIRA ALHALIN MA BASU TABA GANIN JUNA BA
SAI YAU?AKAN WANE DALILI ZAI TSANANTA GABA A
TSAKANINMU HAKA?
Kukasance damu a part 3
In Allah ya kaimu .....
#YusuffSmært
Comments
Post a Comment