sarki dujalu yayi gyaran murya yace sai ku kimtsa kai mai rubutu a ajiye Alkalamimka akan takarda, domin wannan hikayar da zanbaku na dauke da matukar abubuwan Al'ajabi. nikaina ko tinowa nayi da labarin sai nayi kuka. domin wannan hikayace ta wani kyakkyawan saurayi kuma jarumi da ake kira nazmir bin halad dakuma gimbiya luzayya yar sarki bahalubazur A wani zamani can baya da ya shude anyi wata babbar kasa da ake kira duhamul. wannan kasa ta bunkasa girma dakuma karfi da kuma mayaka a bisa wannan dalilin ne kasar duhamul ta shahara kuma ta zama gagara badau acikin duka kasashe kewayanta yazamana ana matukar tsoranta. sarkin duhamul wani azzalumin sarki ne ana kiranshi da bashakur. sarki bashakur ba yaro bane kuma ba tsoho bane domin shekarunsa bazasu gaza arba'in da hudu ba zuwa da biyar (44)_(45) saboda zalunci irin na bashakur ko acikin garin nasa indai mutum bai shafi jinin sarauta ba kokuma bai zamo daya daga cikin attajirai ba to yana cikin tashin hankali domin baka d...