Tapswap code 14 July....

sarki dujalu yayi gyaran murya yace sai ku kimtsa
kai mai rubutu a ajiye Alkalamimka akan takarda, domin wannan hikayar da zanbaku na dauke da matukar abubuwan Al'ajabi.
nikaina ko tinowa nayi da labarin sai nayi kuka.
domin wannan hikayace ta wani kyakkyawan saurayi kuma jarumi da ake kira nazmir bin halad dakuma gimbiya luzayya yar sarki bahalubazur
A wani zamani can baya da ya shude anyi wata babbar kasa da ake kira duhamul.
wannan kasa ta bunkasa girma dakuma karfi da kuma mayaka a bisa wannan dalilin ne kasar duhamul ta shahara kuma ta zama gagara badau acikin duka kasashe kewayanta yazamana ana matukar tsoranta.
sarkin duhamul
wani azzalumin sarki ne ana kiranshi da bashakur.
sarki bashakur ba yaro bane kuma ba tsoho bane
domin shekarunsa bazasu gaza arba'in da hudu ba zuwa da biyar (44)_(45)
saboda zalunci irin na bashakur ko acikin garin nasa indai mutum bai shafi jinin sarauta ba kokuma bai zamo daya daga cikin attajirai ba to yana cikin tashin hankali domin baka da yancin kanka dukiyarka da matanka zasu iya zama na sarki a ko yaushe haka kuma ana daurawa talakawa haraji mai yawa ta yadda ko kadan basa morar arzikinsu
bayan wannan idan sarki bashakur ya bushe iska sai ya tura mayaka zuwa wata kasar
ya basu izinin su murkushe kasan a dibo bayi kuma a dibo dukiyan
bisa wannan dalili ne yatara dukiya mai tsananin yawa wadda shi kansa bai san abinda zaiyi da ita ba.
a wannan zamanin sarki bashakur tsafi baya ya shahara ciki al'umma
babu abinda yafi shahara face karfin dantse da yaki
sarkin yakin wannan bitni da duhamul
wani tsohone dan kimanin shekaru (76)
wanda yayi suna a duniya saboda tsagoran jarumtakarsa
dakuma iya yakinsa a tarihin rayuwarsa ma bai taba jagorantar yaki ansami rashin nasara ba.
Ana kiransa da suna halufa.
Jaafaru ya kara nazarin kayan cikin kifinna yace chab, yau kuma a tsakiyar shuke shuken teku aka watsamu
yanzu taya zamu iya fita dagacikinnan.Nikam banga alamar akwai wata hanya ba.
ko da jin hakan sai gulzum ya bushe da dariyar karfin hali sannan kuma yace amma kacika dakiki kuma kidahumi
waya gayamaka cewa acikin kifi muke
tabbas rayuwarmu na cikin mugun hali domin ko zafin cikin kifinnan bai kashemu ba to kuwa yunwa da kishin ruwa ne zasu kashemu nan da kwanakin da bazasu wuce biyu ba.
ko da jin wannan batu sai gaba dayansu hankalinsu ya dugunzuma kowa ya rasa abinda kemai dadi.
daga can sai yalisa ta dubi masharila tace wai ke ina takamarki ta tsafi take?
mai yasa bazaki cecemu ba daga cikin wannan musiba da muke ciki?
masharila tace ai kinsan cewa gaba da gabanta inda tsafi zai iya ceto mu da tin kafinguguwarnan ta jefomu cikin tekunnan ma zamu kubuta.
jaafaru ya mike tsaye ya dube gaba da baya yajinjina kai yace kai.
amma fa ubangijin da ya alicci wannan kifi ya cika tsoro
koda labari ya iske sarki na sai ya tura aka kirani ya rufeni da fada kuma yace dani lallai a darennan zanzo na yanke kawunanku na kaimasa.
maimakon nayi hakanne na yanke shawarar in kubutar daku.
yakai wannan sarki kayi sani cewar ban kubutar daku domin komai ba saidan naga kanada karama kuma kanada karamar ya wadda kake matukar so itama na fuskanci ta shaku da kai.
don haka ba zanso nazama sanadin raba wannan soyayya ta da da mahaifi ba,
domin nima inada wanda nake matukar so fiye da komai a rayuwa ta, bazanso ace ya zama maraya ba tin yana karami.
Ko da halufa yazonan a zancensa sai kaunarsa ta mamaye zuciyar wannan sarki da jama'arsa
dukkaninsu basusan sa’ar da idanunsu suka ciko da kwalla ba.
nan take sukayi wa halufa godiya sannan sukayi bankwana dashi.
Halufa ya kawo musu dawakai suka haye suka kama gabansu.
tafiyarsu keda wuya sai saurayin ya sauya kayan jikinsa sannan yayiwa kansa raunika a jiki yakoma gidan sarki.
koda sarki bashahur yaga jini na zuba a jikin halufa sai ya mike zumbur ya tareshi cikin firgici yana mai cewa yakai sarkin jarumai mai yafaru gareka.
halufa yace ya shugaba na
Comments
Post a Comment