Mahaifiyar Abba Kabiru Yusuf, ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar NNPP, ta taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Abba Gida Gida ne ya bayyana haka a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis. “Ina karɓar sa albarkar mahaifiyata don murnar cikata shekara 60 a yau. “Ina gode wa kowa da kowa bisa addu’a da goyon baya da ake ba ni. Za mu cim ma nasara tare”, in ji Abba Gida Gida.