Har yanzu gawar Shamsu Muhammad, ɗan Najeriya ɗan asalin jihar Zamfara da aka yi wa kisan gilla a ƙasar Algeria ta na hannun hukumomi da jami'an assibitin ƙasar, domin sun lashi takobin ba za su ba da gawar mamacin ga ƴan uwansa ba har sai ofishin jekadancin Najeriya a Algeria ya saka baki, kuma su basu san ta yadda za su samu ganawa da jekadan na Najeriya a cen ba. Shi dai Shamsu Muhammad ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da aka samu wata hatsaniya tsakanin Hausawa ƴan Najeriya mazauna cen da su ƴan ƙasar, ba shi daga cikin masu faɗan, hasalima shi mai shiga tsakani ne, kuma sunyi nasarar kwantar da tanzomar ta hanyar sulhunta su, to amma bayan lafawar ƙurar wasu matasa suka yi masa dirar mikiya daga baya, a inda suka rufeshi da dukan tsiya har suka farfashe masa kai. Bayan an kwantar da shi assibiti ne rai ya yi halinsa, saboda miyagun raunuka da suka masa. Muna roƙon duk wanda ke da alaƙa ko hanyar da zã a samu ofishin jekadancin Najeriya a Algeria ko lambar da zã a samesu, ya t...