RIJIYA GABA DUBU littafi na daya Part 2 By Yusuff smart ________ Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa tsoho Imzanu yace Abinda yasa nasa maka suna Imhal shine a iya zama na da mahaifiyarka har ta mutu ban taba jin ta ambaci sunan wani mahaluki ba face IMHAL,A kullum duk sanda za taci abinci sai naji tana kiran sunansa tana cewa yazo suci abincin tare,abinda na fahimta shine,koma wanene wannan Imhal din lallai ya kasance babban masoyi a gareta,zai iya kasancewa mijinta ne ko dan uwanta ne ko mahaifinta,Abu na biyu da nake zargi shine,duk yadda akayi mahaifiyarka ta fito daga babban gida domin a ranar da na tsince ta acikin wannan katon ramin mai zurfi sutturar dake jikinta mai matukar tsada ce,babu mai sanya irinta face sarakai da manyan attajirai,babban bakin cikina shine babu wata shaida a tare da mahaifiyarka wadda zata iya sawa a gano asalinta,koda tsoho Imzanu yazo nan a zancensa sai suka sake rungume juna,daga can sai Imhal ya dubi tsoho Imzanu yace,Lallai zan...