– Asiwaju Bola Tinubu ya karyata batun kara aurensa da ya karade ko ina a yanar gizo, inda ya bayyana yadda suke zaune lami lafiya gami da more rayuwar aurensu shi da matarsa – 'Dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, ya kara da cewa, shi bai da niyyar dankaro wa matarsa kishiya, batu ne kawai na masu son janyo rikici cikin iyalinsa – Ya kara da cewa, burinsu ba zai taba cika ba, saboda shi da matarsa a yanzu sun fi mayar da hankali kan fafutukar yakin neman kuri'un don lashe zaben shugaban kasa 'Dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya karyata "Wani labarin kanzon kurege" da ke yawo a yanar gizo cewa zai kara aure, inda ya bayyana yadda yake jindadin rayuwar aurensa da matarsa, Sanata Oluremi Bola Tinubu ya Magantu Kan Rade-Rafin Kara Aure da Ake Yadawa Zai yi. Hoto daga Vanguardngr.news Mai magana da yawunsa, Tundra Rahman ne ya bayyana hakan a wata takarda mai taken,: "Ku Daina Yada Labarin Kanzon Kurege: Asiwaju Bola Tin...